
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ranar yaƙi da jahilci ta duniya a bana ya duba yadda za a inganta ilimin manya
Ranar takwas ga watan Satumban kowacce shekara, rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware, tun a shekarar 1960 a matsayin ranar yaƙi da jahilci, inda ake mayar da hankali wajen faɗakar da jama'ar a sassan duniya mahimmancin ilimi da samar da tsari ko dabarun koyar da mutanen da basu samu dama ba. A mafi yawan ƙasashe dai an sha aiwatar da tsarin yaƙi da jahilci da ke bai wa dattijai ko masu manyan shekaru damar iya koyon rubutu da karatu a rayuwarsu. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

