
Muhallinka Rayuwarka
Matsalar ambaliyar ruwa da ake samu duk lokacin damina a ƙasashen Afrika
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta kowace shekara lokacin damina a sassan ƙasashen Afrika. Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu kasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan kasar. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

