
Episode #16
Fatawowin Rahama: Q&A 30-08-2026 - Prof. Sani R/Lemo
Fatawowin Rahma Ranar Lahadi 17/3/1448 - 30/8/2026 Tambayoyi tare da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON* 1. Wacce hanya mutum zai bi ya zama ɗalibin ilimin hadisi! 2. Wanda ya samu raka’a ta ƙarshe a Sallar Magriba, yaya zai kammala Sallarsa? 3. Hukuncin wanda ya rikice ya kasa tuna raka’a nawa yayi? 4. Lamarin wadda in za ta yi Sallah sai ta ji kamar wani abu zai faɗo mata? 5. Hukuncin mutuwa a wurare masu falala? 6. Laifin wanda ya taimaka wajen zubar da ciki dai dai yake da wanda ya kashe wanda aka haifa? 7. Mutum zai iya yafewa wanda yake bi bashi da ya mutu ba sai ya fadawa iyalan mamacin ba? 8. Ya hallata mutum yayi sadaqa ga iyayensa da suka rasu! 9. Yaya mutum zai sa riba ga kayan da yake sayarwa! 10. Idan aka gina coci a Fili ba tare da izininsa mai filin ba, yaya magada za su yi? 11. Sallar ƙasaru ga matafiyi! 12. In mutum zai cutu a hanyar sa ta zuwa massallaci, zai iya Sallah a gida sannan kuma ya samu ladan wanda ya je massallaci? 13. Mamu zai iya ƙin bin liman da ya hada Sallah in mamun yana ganin sharuɗɗan haɗa sallolin ba su cika ba? 14. Yaya hukuncin Tela da yake aiki a shagon da wutar lantarki da aka janyo zuwa shagon ta sata ce? 15. Akwai addu’ar rufe gida ko daki? 16. Ana iya tofi da shafawa yaro yayin yi masa addu’a safe da yamma? 17. Mace za ita iya Sallah da zani da hijabi da ya rufe jikinta, ko da bata da riga? 18.kashin kaji najasa ne? 19. Hukuncin mutumin da aka bawa bashi da riba amma yake musun haka? 20. Hukuncin Wucewa gaban mamu ta kofar da aka bar ta a bude domin wucewar mutane! 21. Mace za ta iya Sujjadar Tilawa ba tare da hijabi ba? 22. Mutum zai iya azumin domin ya samu lada sannan ya rage kiba? 23. Mutumin da yayi alwala, yayi Azkar din bacci sannan ya sadu da iyalansa, sai ya sake Azkar? 24. Mutumin da yake Sallar dare, an ina ya kamata yayi addu’oinsa? 25. Yaya ya kamata musulmi ya gaishe da manya? 26. Akwai hadisin da ya ce za a fara sahu daga tsakiyar sahu?






